Siyasa
Na sauya sheƙa zuwa NNPP- Abdulmumin Jibril Kofa
Tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji Abdulmumin Jibril Kofa, ya sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP.
Tsohon ɗan majalisar ya sanar ya bayyana barin jam’iyyar ta APC ne a shafukansa na sada zumunta a daren Lahadi nan.
Haka kuma ya ce ya koma jam’iyyar ta NNPP ne tare da dukkan magoya bayansa.
Abdulmumin Jibril Kofa, ya kuma ce, tuni suka karɓi katin shaidar zama ƴan jam’iyyar NNPP a gidansa dake garin kofa, a karamar hukumar Bebeji.
