Tsaro
Kano: Ƴan bindiga sun kashe mutane 6 tare da sace Dagaci
Shafin Jaridar Solacebase Hausa ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi, lokacin da ɓata garin suka kutsa garin tare da yin harbi kan mai uwa da wabi inda suka harbi mutum 9.
Haka kuma jaridar ta ruwaito cewa mutane 6 sun mutu yayin da 3 kuma suke cikin mawuyaci hali.
Bayan nan ne kuma suka sace Dagacin yankin tare da arcewa da shi.
Haka kuma Solacebase ta ruwaito cewa, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa, tuni suka duƙufa wajen ceto Dagacin.
