Labarai
Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 4 a fashewar gas ɗin Sabon Gari
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, mutane 4 ne suka mutu a fashewar tukunyar iskar gas da ta faru a unguwar Sabon Gari da safiyar yau Talata.
Kwamishinan ƴan sandan Kano Sama’ila Shu’aibu Dikko, ne ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.
Kwamishinan ya ce, tukunyar gas ɗin ta fashe ne a wurin walda kusa da makarantar firamare ta Winners Kids Academy a titin Aba da ke yankin.
Dikko ya kuma ce, masu aikin ceto suna ci gaba da ƙoƙarin gano mutanen da suka makale a ƙarƙashin ginin wurin wanda ya rufta sakamakon fashewar.
Haka kuma kwamishinan ƴan sandan ya buƙaci al’ummar jihar Kano, da su kwantar da hankula bisa faruwar lamarin.
Dikko ya kuma ƙaryata rahoton da ake yaɗawa cewa Bom ne ya fashe yana mai cewa labarin ƙanzon Kurege ne.
