Kasuwanci
Dala ta yi tashin gwauron zabi a kan Naira
A Karon farko Dalar Amurka ta yi tashin gwauron zabi a kan Naira inda a yau Lahadi dalar ta kai kimanin Naira ɗari shida da goma a kuɗin Najeriya a kasuwar bayan fage.
Solacebase ta ruwaito cewa, Duk da cewa farashin naira a hukumance kowacce ɗaya tana dai-dai da Naira ɗari huɗu da sha tara da kwabo biyu, sai dai a yau ana musayarta a kan wannan adadi.
Haka kuma ta ƙara da cewa wani kamfanin canji kuɗi mai suna Aboki Forex, wanda ke da shafin yanar gizo da ƴan Najeriya ke sanin farashin canjin kuɗin ƙasashen ke tare daga shi a kan farashin bayan fage, ya ruwaito cewa ana sayar da Dala kan Naira 610 a safiyar yau Lahadi.
Tun a ƴan watannin baya ne dai Naira ke ci gaba da faɗuwa matuƙar idan aka kwatanta ta da Dala.
A baya-bayan nan an samu tashin dalar daga Naira 588 kan kowacce Dala guda a ranar 8 ga wannan wata da muke ciki na Mayu, inda kuma a yau ɗin aka buɗe hada-hadarta a kan Naira 610 a cewar Aboki Forex.
