Labarai
Shugaba Buhari ya ziyarci jihar Kano
A yau Litinin ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano domin wata ziyarar aiki.
Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa jirgin shugaban ƙasar ya sauka ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Haka kuma ta ce, gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya tarbi shugaba Buhari da ministocinsa tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.
