Labarai
CBN ya musanta sauke Emefiele daga muƙaminsa
Babban bankin Najeriya CBN, ya ƙaryata labarin da wasu kafafen yaɗa labaran Internet suka yaɗa wanda ke cewa gwamnatin tarayya ta sauke gwamnan banking Mista Godwin Emefiele.
Shugaban sashen yaɗa labarai na babban bankin Mista Osita Nwanisiobi ne ya bayyana hakan ranar Larabar a Abuja lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Haka kuma ya ce, yanzu haka Emefiele yana kasar waje domin ziyarar aiki a hukumance.
