Labarai
Mataimakin gwamnan Zamfara da aka tsige ya janye daga takarar gwamna
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara da aka tsige shi a baya-bayan nan, kuma mai neman takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP a zaɓen baɗi Barista Mahdi Aliyu Gusau, ya sanar da janyewa daga takarar.
Barista Mahdi Aliyu, ya sanar da hakan ne yau Laraba a Gusau babban birnin jihar bayan da jam’iyyar ta fara gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnoni.
Haka kuma ya buƙaci magoya baya da wakilansa da shugabannin jam’iyyar kan su zaɓi Dakta Dauda Lawal Dare don ya samu tikitin takarar.
Solacebase ta ruwaito cewa tsohon mataimakin gwamnan, ya godewa magoya bayansa kan irin goyon bayan da suke ba shi daga lokacin da yake mataimakin gwamna har zuwa yanzu.
