Siyasa
Mustapha Sule Lamido ya zama ɗan takarar gwamnan Jigawa a jam’iyyar PDP
Alhaji Mustafa Sule Lamido, ɗa ga tsohon gwamna Sule Lamido na Jigawa, ya samu tikitin zama ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarkashin jam’iyyar PDP a zaɓen baɗi.
Jami’in kula da masu kada kuri’a na zaben Malam Isah Ahmed, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayyana sakamakon zaɓen yau Laraba a Dutse babban birnin jihar.
Jami’in ya ce, Mustafa Lamido, ya samu nasara ne da ƙuri’u 829 daga cikin kuri’u 832 da aka kaɗa.
Haka kuma ƙara da cewa, Alhaji Saleh Shehu ne ya zo na biyu, amma bai samu ƙuri’a ko ɗaya ba.
Malam Isah Ahmed, ya kuma taya wanda ya lashe zaɓen da wakilan jam’iyyar da kuma ƴaƴan jam’iyyar murna bisa yadda suka gudanar da shi cikin nasara da lumana.
A nasa ɓangaren, Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Babandi Ibrahim, ya ce jam’iyyar za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen gabatar da sahihin dan takarar kujerar gwamna a jihar, wanda zai taimaka wajen dawo da martabar jihar.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa guda cikin masu neman tsayawa takarar gwamnan jihar Alhaji Adamu Bashir ya sanar da janyewarsa sa’o’i kaɗan kafin fara zaɓen fitar da gwanin.
