Connect with us

Labarai

Ƙungiyar NUJ reshen ARTV ta kafa kwamitoci 3 domin samar da ci gaba a tashar

Ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya NUJ reshen tashar talabijin ta ARTV Kano, ya kafa kwamitoci uku domin samar wa mambobinta ci gaba mai ɗorewa.

Hakan na cikin wata sanarwa da mataimakin sakataren ƙungiyar Naziru Idris Ya’u ya fitar bayan kammala taron da shugaban kungiyar Abubakar Shehu Kwaru ya jagoranta.

Sanarwar ta ce, yayin zaman an tattauna batutuwa da dama da suka shafi ƙungiyar musamman ma ga ɓangaren ɗakin labarai inda suka jaddada buƙatar daukacin mambobin ƙungiyar su sanya hannu a kai da nufin tabbatar da kwazo a aikinsu.

Kwamitocin uku sun haɗa da kwamitin kuɗii wanda Mubarak Ismail Abubakar Madungurum zai jagoranta, Farida Umar Abdu a matsayin sakatariyar kwamitin da Zulfa’at Abubakar Rano a matsayin mamba.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, An kafa kwamiti na biyu domin tsara kalandar kungiyar ƙarkashin jagorancin Alhaji Ado Salisu da Naziru Idris Ya’u a matsayin Sakatare da Abdullahi Hassan da Umma Adamu Abubakar da Zulfa’at Abubakar Rano a matsayin mambobin kwamitin.

Sai Kwamitin na uku da ƙungiyar ta kafa domin gudanar da bincike kan matsalolin da ɗakin labarai da nufin sanya kawo gyara, wanda Kwamared Rabi’u Aboki Ana’s zai jagoranta sai kuma Malam Nasiru Yusuf Ibrahim a matsayin Sakatare tare da Hafsat Sani Usman da Kwamared Sabo Yahaya Aliyu da Zulfa ‘ Abubakar Rano a matsayin mambobin kwamitin.

Bayan kafa kwamitocin guda uku, Kwamared Abubakar Shehu Kwaru ya yi kira ga kwamitocin da su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu, inda ya ce an zaɓo dukkan shugabanni da mambobin kwamitocin ne bisa cancantar su tare da umartarsu da su yi aiki tare domin ciyar da kungiyar gaba har ma da tashar baki ɗaya.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, Shugaban ƙungiyar ya ci gaba da yin amfani da wannan damar wajen miƙa godiyarsa ga mahukuntan gidan talabijin ɗin na ARTV Kano karkashin jagorancin Hajiya Sa’a Ibrahim bisa goyon baya da jagoranci wajen samun nasarar kafuwar sababbin shugabannin.

Yayin ƙarƙare taron Kwamared Abubakar Shehu Kwaru, ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su yi watsi da dukkan abubuwan da za su haifar da rashin hadin kai a tsakanin su, maimakon haka ya buƙace su da su haɗa kai domin bunkasar ƙungiyar tasu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet