Labarai
Kano: Masu garkuwa da mutane sun sace mahaifiyar A. A Zaura
Wasu ɓata gari da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun yi sace mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Abdulsalam Abdulkarim da aka fi sani da A.A Zaura.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa an sace mahaifiyar ɗan takarar ne Hajiya Laure Mai Kunu da Asubahin yau Litinin.
Haka kuma jaridar ta ce, shugaban ƙaramar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, ne ya tabbatar mata da faruwar lamarin yana mai cewa jami’an tsaro ne suka rahoton sace dattijuwar a gidanta da ke mazaɓar Rangaza a ƙauyen Zaura na karamar hukumar.
Haka kuma jaridar ta ruwaito cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, har ma ya ce, tuni an tura tawagar ƴan sanda ta Operation Puff Adder domin kuɓutar da ita tare da cafke waɗanda ake zargi da sace ta.
