Labarai
Malam Shekarau ya zama ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya
Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau, ya tikitin yin takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP.
Sanatan dai ya samu nasarar ne bayan kammala zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar wanda da aka gudanar a ƙaramar hukumar Gezawa.
Yayin zaɓen, Malam Ibrahim Shekarau, ya samu nasarar ne da ƙuri’u 516.
A baya-bayan nan ne Sanatan ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.
