Labarai
Jami’an DSS sun kuɓutar da mahaifiyar A. A Zaura
Jami’an hukumar tsaro ta DSS, sun samu nasarar kuɓutar da Hajiya Laure, mahaifiyar ɗan takarar kujerar Sanatan mazaɓar Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC A. A Zaura.
Rahotonni sun bayyana cewa jami’an sun ceto dattijuwar ne bayan da ta kwashe fiye da sa’o’i 24 a hannun ɓata garin da suka yi garkuwa da ita.
A cikin daren Lahadin da ta gabata ne ƴan ta’addar suka kutsa kai cikin gidanta da ke mazaɓar Rangaza a ƙauyen Zaura da ke yankin ƙaramar hukumar Ungogo inda suka arce da ita.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Ungogo Engr Abdullahi Garba Ramat ne ya tabbatar da kuɓutar mahaifiyar ɗan takarar yana mai cewa an ceto ta ne a jihar Jigawa.
