Siyasa
Tinubu ne ke kan gaba a ƙuri’un da aka tantace
Jagoran jam’iyyar APC kuma ɗan takara a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ne ke kan gaba da yawan ƙuri’un da aka soma ƙidayawa domin tantance yawan kuri’un da kowanne ɗan takara ya samu.
Sauran wadanda suka samu ƙuri’a a wannan tantacewa sun haɗa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da Rotimi Amaechi da Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Ana dai kan tantace kuri’un da daliget 2,340 suka kaɗa.
Da misalin karfe 2:40 na daren jiya Talata ne aka soma zaɓe har zuwa 8 na safen yau Laraba.
