Connect with us

Featured

An Naɗa Sabon Dagacin Garin Kundila Dake Karamar Hukumar Shanono

Masarautar Ƙaraye ta naɗa sabon Dagaci biyo bayan murabus da tsohon Dagacin ya yi saboda shekarun tsufa.

Mai martaba sarkin Karaye Alhaji DR. Ibrahim Abubakar II ne ya naɗa Alhaji Halilu Ibrahim a matsayin sabon dagacin garin Kundila dake ƙaramar hukumar Shanono ta Jahar Kano.

Halilu Ibrahim ya gaji mahaifin sa ne wanda ya yi murabus sakamakon shekarun tsufa.

Wannan dai na ƙunshe ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na masarautar Karaye Haruna Gunduwawa, kuma ya raba wa manema labarai a ranar Laraba .

An haifi sabon dagacin  a watan Augustan shekarar 1964 a Garin Kundila, wanda ya samu shaidar karatunsa na Digiri a jami’ar Bayero dake Kano a fannin ilimin tarihi da kuma harshen Hausa, kazalika ya yi wasu kwasa-kwasai  a fannonin ilimi daban-daban a fadin ƙasar nan.

Al’umma da dama sun yaba da dabi’un sabon dagacin na su, da cewar mutumin kirkine kuma jajirtacce.

Tuni dai hukumar da ta ke yaƙi da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi masa gwaji inda ta tabbatar da cewa baya ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Da yake jawabinsa bayan naɗin mai martaba sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar Ii ya taya sabon dagacin murna tare da kira gareshi ya zamo mai riƙon gaskiya da kuma riƙe amanar da aka ɗora masa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet