Siyasa
Da ɗumi-ɗumi: Sanata Adamu Aleiro ya sauya sheƙa zuwa PDP
Tsohon gwamnan jahar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Tsohon gwamnan wanda yanzu haka ɗan majalisar dattawa ne, ya bayyana ficewar tasa ne yau Alhamis a Birnin Kebbi.
Sanatan ya ce, ya ɗauki matakin sauyin sheƙar ne domin cika burin magoya bayansa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, gaban in fitar tasa sai da ya yi ƙoƙarin ganin an samu daidaito tsakanin sa da uwar jam’iyyar APC ta jihar Kebbi dangane da saɓa in da ke tsakaninsu, sai dai hakan ba ta samu ba.
