Connect with us

Featured

Dubun Wasu Matasa Ta Cika Yayin Da Suka Je Yin Kashedi Ga Mahaifin Wata Budurwa

Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta tabbatar da cafke wasu matasa 3 da ake zarginsu da zuwa ƙaramar hukumar Rimin-Gado ta jahar Kano, sanye da kayan soja da na yan bijilanti harma da wanda yake kiran kansa da jami’in kare haƙƙin dan Adam.

Matasan sun hada da Umar Yakubu Rafin Kuka da Hassan Shu’aibu Rafin Kuka da Abdul’ziz Musa Sheka, wadanda suke je garin domin yin kashedi ga mahaifin wata budurwa Mallam Haruna Inuwa, sakamakon an shaida masa cewar abokin su ne yake sonta .

Mahaifin Budurwar Haruna Inuwa ya bayyana cewa matasan sun zo da misalin karfe 11:00pm na dare.

Haruna ya ƙara da cewar ya bayar da yarinyar ga wani kuma wanda aka bata bata sonsa abokin sa take so.

Su ma matasan sun bayyana cewa Umar ne ya gayyace su domin suje su yi sulhu da mahaifin budurwar sakamakon bata wanda bata so.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun samu kiran gaggawa daga chaji ofis ɗin  karamar hukumar Rimin-Gado a ranar 6 ga watan da muke ciki da cewar mutanan garin sun kama wasu matasa da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, inda aka mika su ga hannun jami’an tsaro.

Kiyawa ya ƙara da cewa daya yana sanye da kayan sojoji, wani yana sanye da kayan Bijilanti sai kuma wanda ya ce shi jami’in kare haƙƙin dan Adam ne.

Yanzu haka dai kwamishinan ƴan sandan jahar Kano Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayar da umarnin  dawo da su babban sashin gudanar da bincike na aikata manyan laifuka dake Bompai a Kano.

Kiyawa ya kuma ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet