Kasuwanci
Shugaba Buhari ya ƙaddamar da shirin tattalin arziki ta fasahar Internet
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da shirin tattalin arziki Najeriya ta hanyar fasahar internet.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Shugaba Buhari, ya kaddamar da sabon shirin ne a ƙarkashin ministan sadarwa da tattalin arzikin fasaha Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, da zai jagoranci tsarin.
Yayin ƙaddamarwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙara ƙaimi wajen ƙara haɓɓaka fasahar Internet domin samun gwaggwaɓar riba da ƙara bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
Shirin dai, na ƙarƙashin wani kwamitin wanda shugaba Buhari ya kafa.
