Labarai
Kotun ƙoli ta bai wa ɗalibai mata damar sanya hijabi
Kotun ƙoli a jihar Lagos, ta yanke wani hukunci wanda ya bai wa ɗalibai mata musulmi damar su sanya hijabi a makarantun jihar Lagos ba tare da nuna musu tsangwama ba.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a birnin tarayya Abuja yau Juma’a.
Tun a watan Oktoban shekarar 2014 wata babbar kotun tarayya da ke Lagos ta yanke hukuncin hana sanya hijabi a makarantu, wanda a watan Yuli 2016 aka daukaka kara.
BBC ta ruwaito cewa hukuncin na yau zai kawo ƙarshen dambarwar da aka dauki tsawon shekaru ana yi kan amfani da hijabi a marantu ga dalibai Musulmi.
