Labarai
Allah ya yi wa Tsohon gwamna Kanal Musa Shehu rasuwa
Allah ya yi wa tsohon gwamnan jihohin Ribas da Filato a mulkin soja Kanal Musa Sheikh Shehu mai ritaya rasuwa.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa wata majiya mai tushe ta shaida mata cewa, marigayin ya rasu ne da safiyar yau Lahadi.
Marigayin ɗan asalin jihar Sokoto, ya yi mulki a Jihar Ribas, daga watan Agustan shekerar 1996 zuwa Agusta 1998 a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha.
Haka kuma ya mulki jihar Filato har zuwa lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya a watan Mayun shekerar 1999.
A shekarar 2010 kuwa marigayi Kanal Musa Shehu ya kasance a matsayin babban sakataren kungiyar tuntuɓa ta Arewa watau Arewa Consultative Forum ACF.
