Labarai
Gwamnatin El-Rufai ta sake korar Malamai 2,357
Hukumar kula da ilimin bai-ɗaya ta jihar Kaduna KADSUBEB, ta sanar da sake korar malaman makaranta kimanin dubu biyu da ɗari uku da hamsin da bakwai.
Mai magana da yawun hukumar Hauwa Mohammed ce ta bayyana haka ta cikin sanarwar da ta fitar jiya Lahadi.
Sanarwar ta ruwaito cewa, an salami malaman 2,357 ne bisa faɗuwa da suka yi a jarabawar da gwamnatin jihar ta shirya musu a watan Disamban bara.
Haka kuma ta ƙara da cewa, an shirya jarabawar ne ga malamai fiye da su dubu talatin.
Sanarwar ta ƙara da cewa, cikin malaman firamare 2,192 da aka kora har da shugaban ƙungiyar malamai ta Najeriya NUT Audu Amba, bisa ƙin rubuta jarrabawar da ya yi.
Hukumar ta ƙara da cewa, n kuma sallami malamai 165 daga cikin 27,662 da suka rubuta jarabawar waɗanda su kuma an kore su ne saboda rashin ƙoƙari.
Hauwa Mohammed ta cikin sanarwar ta ƙara da cewa “Ba mu da buƙatar malaman da suka sami ƙasa da maki 40 cikin 100 a jawabawar, don haka kore su daga aiki.”
“Malaman da suka samu kaso 75 cikin 100 su aka tantance a kuma mun bayyana su a matsayin kwararru kuma sun cancanta su koyar kuma za su fara zuwa kwasa-kwasai kan shugabanci da gudanarwar makarantu,” inji ta.
