Connect with us

Featured

Rotimi Amaechi Ne Ya Cancanci Zama Ministan Sufuri – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce Amaechi na bukatar kammala ayyukan jiragen kasa da ake gudanarwa a fadin kasar nan.

“Ya kamata a mayar da shi don tabbatar da cewa wadannan kwangilolin da aka kulla da China da Portugal da sauran masu kudi na ayyukan layin dogo, a kalla ya gansu har karshe,” in ji Sani a wata hira da gidan talabijin na Channels ta cikin shirin Politics today.

Ya cigaba da cewa “Saboda al’ada ce a kasar nan, duk lokacin da aka samu sabon minista, yawanci ayyuka suna tsayawa ne lokacin da ya kamata a ci gaba da gudanar da mulki da ayyukan gwamnati.”

Tsohon sanatan ya bayyana cewa ayyukan layin dogo na bukatar a samu shugaban da zai ci gaba da tafiyar da kwangilolinsu domin cimma burin da aka sa gaba.

Da yake bayyana ma’aikatar sufuri a matsayin mai matukar muhimmanci, jigon na PDP ya ce tsohon ministan ya yi alkawarin kammala dukkan ayyukan jiragen kasa kafin karewar wa’adin Buhari a 2023.

Ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin mai ci, yana mai cewa abubuwa suna yin tafiyar hawainiya a gwamnatin.

Sani ya ce akan dauki lokaci mai tsawo kafin shugaban kasa ya maye gurbin ministocin da suka yi murabus, yana mai tuna yadda Buhari ya jinkirta nada mambobin majalisarsa a 2015.

Ya kara da cewa, “A bisa ka’ida, idan aka samu gibi na murabus din ministocin da shigarsu fagen siyasa, ya zama wajibi ga shugaban kasa ya nada sabbin ministocin da za su ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati da gudanar da mulki kamar yadda aka saba.

A baya dai shugaba Buhari ya aike da sunayen mutane bakwai ga majalisar dattawa a matsayin wadanda za su maye gurbin ministocin da suka yi murabus domin cimma burinsu na siyasa.

Wadanda murabus din ya shafa sun hada da Amaechi, Ogbonnaya Onu (Kimiyya da Fasaha) Godswill Akpabio, (Al’amuran Neja Delta), da Emeka Nwajiuba (Ilimi, Jiha).

A yayin da suka bar aikinsu na neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Uche Ogah, ya fice daga matsayinsa na karamin ministan ma’adinai da karafa don neman takarar gwamnan Abia.

Hakazalika, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Tayo Alasoadura, shi ma ya yi murabus don neman tikitin takarar sanata na APC a Ondo.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet