Featured
Kotu Ta Yankewa Wani Dan Kasuwa Hukuncin Daurin Shekaru Bakwai A Gidan Kaso
Wani dan kasuwa mai suna Jamilu Sule da ke Kano an yanke masa hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari ba tare da wani zabin tara ba, biyo bayan wata kara da aka shigar akansa na samun kadarori wanda suka kai Naira 7, 677,000 bisa zargin karya.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta (EFCC) shiyyar Kano ta gurfanar da Sule a ranar Laraba, a gaban mai shari’a Dije Abdu Aboki na babbar kotun jihar Kano, bisa tuhumarsa da ake masa na samunsu ta hanyar karya.
A cewar wata sanarwa da kakakinta, Tony Orilade ya fitar, a lokacin shari’ar farko da ta yi a shekarar 2019, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ana zargin Sule ne da karbar kayayyakin da darajarsu ta kai Naira 7,677,000 a kan bashi da sunan cewa zai kai su ga manyan kantuna.
“Binciken da Hukumar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake tuhuma yana da dabi’ar tattara kaya da sunan kai su manyan kantuna, amma zai karkatar da kayan don amfanin kansa,” in ji sanarwar.
‘’Hukumar ta kuma bayyana cewa ta gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Dije Aboki a kan tuhume-tuhume hudu na samun kudi ta hanyar karya.

Mutumin da ake yankewa hukuncin daurin shekaru 7
Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce: “Kai Jamilu Sule, tsakanin Yuli zuwa Agusta 2018 a Kasuwar Singer Kano, da ke karkashin ikon wannan kotu mai daraja, ana tuhumarka da yin zamba, da yaudara, da samu wasu kayayyaki da kayan abinci na Naira 7,677,000 kadarorin mallaki Mohammed Shariff Ahmad, Ibrahim Dauda Abdullahi da Tajuddeen Abdulrahaman, ka aikata laifin damfara a kan wadannan kayayyaki, inda ka aikata laifin da ya sabawa sashe na 320 na kundin laifuffuka da kuma hukunci a karkashin sashe na 322 na wannan doka.”
An fara gurfanar da Sule ne a ranar 21 ga watan Mayu, 2019, kuma ya ki amsa laifuffuka hudu da EFCC ta gabatar masa.
A yayin shari’ar, lauyan mai shigar da kara, Micheal Ojo, ya kira shaidu 4 tare da rufe kararsa.
