Labarai
Bauchi: Ƴan sanda sun cafke mutane 3 bisa zargin cire wa yaro Ido
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, ta ce, ta kama wasu mutane uku bisa zarginsu da ƙwaƙule wa wani yaro ɗan shekaru goma sha shida idanu domin haɗa layar ɓata.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Ahmed Wakili ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.
Ya ce, cikin mutanen da rundunar ta cafke har da wani boka wanda ke yin amfani da sassan jikin mutane wajen yin tsafi.
A makon da ya gabata ne dai aka yi zargin cewa wasu mutane sun yaudari yaron tare da kai shi cikin daji inda suka ƙwaƙule masa idanun.
