Labarai
Kaduna: Ƴan bindiga sun sace sabon DPO
Rahotonni daga jihar Kaduna sun tabbatar da cewa, Ƴan bindiga, sun sace wani sabon Baturen ƴan sanda watau DPO na yankin Birnin Gwari.
Lamarin dai ya faru ne kwanaki huɗu da sace wani DPO a jihar Nasarawa.
Jaridar Solacebase ta ruwaito, an sace jami’in ne a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar yau Litinin.
Haka kuma ta ce, an sace Baturen ƴan sandan ne a hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari domin kai wani rahoto.
Jaridar ta ƙara da cewa, har zuwa bayan 11:00 na daren nan da ta fitar da rahoton rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba magantu ba kan lamarin, kuma ko da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar Mohammed Jalinge, cewa ya yi za su magantu a gaba.
