Connect with us

Labarai

Jigawa: Ƴan kai amarya 6 sun mutu a hatsarin mota

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wani direba da mata da ƙananan yara a hanyar su ta komawa hadejia daga kai amarya.

Rundunar ta bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta DSP Lawan Shisu Adamu.

Aka kuma sanarwar ta bayyana cewa, mutane shida ne suka mutu a hatsarin tare da jikkatar ƙarin wasu mutanen uku.

Rundunar ta cikin sanarwar ta ce, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:20 na daren ranar 26 ga wannan wata na Yuni da muke ciki.

Ta ce, hatsarin ya faru ne lokacin da direban motar kirar Lexus baƙa mai lamba AAA 153 EA wadda Habib Habib Tall mai shekaru 30 ke tuƙawa ɗan garin Yalleman a ƙaramar hukumar Kaugama sakamakon cirewa tayoyin motar guda biyu lokacin da yake tsaka da gudu.

Haka kuma sanarwar ta ce, hatsarin ya faru ne a Gidan Sugar,inda bayan samun rahoto ƴan sanda suka garzaya wurin tare da miƙa su Babban Asibitin Hadejia a nan ne likitoci suka tabbatar da mutuwar mutanen 6 ukun kuma suna kan karɓar magani.

Rundunar ƴan sandan ta Jigawa, ta bayyana sunayen waɗanda suka rasu kamar haka:- Baba Rabi’a Aliyu mai shekaru 50 da Ummi Abubakar mai shekaru shekara 30 da Aisha Soja mai shekara 27 da Radiya Turaki ƴar shekaru sai Kabir Sani mai shekara 2 da rabi da kuma Habib Habib Tall mai shekaru 30.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet