Connect with us

Labarai

Katsina: Yunwa ta kashe ƴan gudun hijira 22

Rahotonni daga jihar Katsina na nuni da cewa, Kimanin mazauna sansanin ƴan gudun hijira 22 ne suka mutu sakamakon fama da yunwa.

BBC ta ruwaito cewa mutanen sun mutu ne a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke yankin ƙaramar hukumar Jibiya.

Haka kuma ta ruwaito cewa sansanin na ɗauke da dumbin ƴan gudun hijira da suka tsere daga garuruwan jihar ta Katsina sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro.

Akwai kimanin ƴan gudun hijira har mutum dubu goma sha biyar waɗanda suka fito daga garuruwan Shimfida, da Zango da Kwari da Tsembe da Tsauni da kuma Mai Wuya.

A cewar shugaban sansanin Malam Sa’ad Salisu Shimfida, an samu ƙaruwar baƙi da dama a sansanin kuma ba tare da an ƙara musu yawan abincin da ake basu ba wanda ya alaƙa ta hakan a matsayin musabbabin mutuwar tasu.

“Dalilin haka yara da dama da wasu mutanen suka mutu” in ji shi.

“Akwai ƙarancin abin shimfida, da yawa a ƙasa suke kwana, ga shi babu maganin sauro da na ƙwari duk babu.”

Haka kuma, BBC ta ce ko da ta tuntubi shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Alhaji Babangida Nasamu ya musanta zargin.

Ya ce, “Ni da ma’aikatanmu na SEMA mun mayar da Jibiya kamar gida, kusan ko yaushe muna can kuma kullum muna magana da shugaban ƙaramar hukumar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a yanzu haka gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya ba da miliyan 100 don a tsugunar da ƴan gudun hijirar, kuma ana wadata su da abinci sosai.

Sai dai dama jihar Katsinan na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a arewacin kasar musamman ma satar jama’a, kuma akwai yan jihar da dama da ke gudun hijira a kwaryar birnin jihar, da kuma wasu jihohi makwabta kamar yadda ƙafar ta ruwaito.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet