Zamantakewa
Rana bata ƙarya: Yau ce ranar da majalisar dattawa ta sanya domin tantance mutanen da Buhari zai naɗa Ministoci
A yau Laraba ake sa ran majalisar dattawa za ta tantance mutanen da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya aike wa majalisar domin tantancewa gaban in naɗinsu a matsayin ministoci.
A makon jiya ne yayin ɗage zaman majalisar shugabanta Sanata Ahamad Lawan, ya ce, majalisar za ta tantance mutanen a ranar Laraba 29 ga wannan wata na na Yuni.
Tun a baya dai, Shugaba Buhari ya aike wa majalisa takarda mai ɗauke da kwanan wata 15 ga watan Yuni inda ya tura sunayen mutanen da za a tantance ɗin.
Mutanen dai sun haɗa da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano da Umana Okon Umana daga Akwa Ibom da Henry Ikechukwu Iko daga jihar Abia.
Sauran sun haɗa da Ademola Adegoroye ɗan asalin jihar Ondo da kuma Odum Odi daga jihar Rivers da Goodluck Nnana Opia daga Imo da kuma Joseph Ukama daga jihar Ebonyi.
