Labarai
Wasu Fusatattun Sanatoci Sun Gana Da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Abuja
Wasu Sanatoci da suka fusata a dandalin jam’iyyar (APC) sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja ranar Talata.
Sanatocin wadanda adadinsu ya kai 22, sun yi alkawarin ficewa daga jam’iyyar ne sakamakon zaben fidda gwani na jihar su gabanin babban zaben 2023.
Shugaban tawagar, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce ‘yan majalisar na ganin ba a basu hakkinsu a tsarin ba.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaba Buhari ya bukaci Sanatocin da su yi hattara a matakin ficewa daga jam’iyyar.
‘Yan majalisar APC da dama sun sauya sheka kwanan nan.
Shugaba Buhari ya ce sauya shekar barazana ce ga rinjayen jam’iyyar APC a majalisar dokokin kasar.
Bayan kammala taron, Kalu ya ce Sanatocin da suka fusata ba za su sake komawa APC ba.
“Da yammacin yau, na jagoranci Sanatoci 22 da ke cikin fushi da yan jam’iyyar APC zuwa wajen shugaban kasa Muhammad Buhari, GCFR,” Kalu, babban mai ba da shawara na majalisar dattawa ta tara, a cikin wata sanarwa.
” Ganawar da muka yi da shugaban kasa ta yi nasara kuma batun sauya sheka daga jam’iyyarmu an barshi.”
