Labarai
Wata Kotu A Kano Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Daga Karbo Bashin Biliyan 10 Don Siyan CCTV
A ranar Juma’a nan ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Liman, ta hana gwamnatin jihar Kano rancen naira biliyan 10 domin sanya na’urar daukar hoto ta Closed-Circuit Television (CCTV).
Gamayyar kungiyoyi masu kishin Kano, ta Kano First Forum (KFF) ta shigar da kara mai dauke da kwanan wata 27 ga watan Yuni, wanda Darakta Janar na kungiyar Dakta Yusuf Isyaka-Rabiu ya jagoranta
KFF ta bakin lauyanta, karkashin jagorancin Badamasi Suleiman-Gandu, ta roki kotun da ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano rancen Naira biliyan 10.
KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa, a ranar 15 ga watan Yuni, 2022, Majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da bukatar gwamnan na karbar bashin Naira biliyan 10 daga bankin Access.
Sauran wadanda ake kara a karar sun hada da Babban Lauyan Jihar Kano, Kwamishinan Kudi na Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Sauran sun hada da Bankin Access, Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Ofishin Kula da Bashi da Hukumar Kula da Kudi.
Mai shari’a Liman ya amince da rokon kungiyar KFF tare da hana wanda ake kara na farko cin bashin Naira biliyan 10 sannan ya umarci dukkan bangarorin da su ci gaba da kasancewa a yanda ake.
Ya kuma umurci wadanda aka shigar kara ma’aikatar kudi ta tarayya, ofishin kula da basussuka da hukumar kula da kasafin kudi da su bi umarnin kotu.
Solacebase ta rahoto cewa KFF na kalubalantar Gwamnan Jihar Kano kan karbo bashin Naira biliyan 10 bisa dalilan rashin bin ka’idojin rance.
Masu neman a cikin rokonu sun kalubalanci gwamnatin jihar ba tare da bin dokar kafa ofishin kula da basussuka ta 2003 da dokar kasafin kudi ta 2007 da kuma dokokin jihar Kano na 1968 ba bisa ka’ida ba, ba su da tushe balle makama.
Majalisar dokokin jihar a ranar 15 ga watan Yuni ta amince da bukatar Ganduje na neman Naira biliyan 10 daga bankin Access.
