Shugaban Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya bayyana cewa sojoji za su janye su bada dama ga gwamnatin farar hula.
BBC ta ruwaito cewa shugaban ya bayyana hakan ne ta cikin wani jawabi da ya a talabijin.
Ya ce, sojoji ba su shiga sha’anin miƙa mulki ga farar hula ba, kuma a shirye suke su tabbatar da an yi sahihin zaɓe.
Kafar ta ƙara da cewa, Masu rajin tabbatar da dimokuraɗiyya sun shafe kwanaki suna gudanar da zanga-zanga a sassan ƙasar domin neman kawo ƙarshen mulkin soji.
A baya, Janar Burhan ya yi watsi da kudirin miƙa mulki ga farar hula.
