Connect with us

Labarai

Masarautar Katsina Ta Dakatar Da Bukukuwan Hawan Babbar Sallah A Bana

Majalisar Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da hawa a lokacin bukukuwan babbar Sallah (Eid-el-Kabir) a ranar Asabar.

Sanarwar dakatarwar ta fito ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Katsina, ta hannun mataimakin sakataren majalisar, Alhaji Sule Mamman-Dee.

Ya ce an dakatar da aikin ne saboda yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar.

A cewar Mamman-Dee, Sarkin, Alhaji Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna matukar damuwarsa kan matsalar tsaro a sassan masarautar, inda ya ce zai halarci Sallar Idi ne kawai a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa Sarkin ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Bikin hawan Durbar dai ya samo asali ne tun shekaru aru aru, kuma ya kunshi baje kolin fasahar hawan doki daga gundumomi da masu fada aji, wadanda suke yi wa Sarkin Mubaya’a a ranar Idi da aka fi sani da ‘Hawan Daushe’ a Katsina.

A nasa bangaren, Sarkin zai jagoranci tawagar ‘yan majalisar masarauta da hakimai da kauye a cikin jerin gwanon dawaki da aka fi sani da ‘Hawan Bariki’ domin yin mubaya’a ga gwamnan jihar, kwana guda bayan kammala Idi. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet