Connect with us

Siyasa

Sanata Uba Sani ya zaɓi Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokin yar takara

Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Uba Sani, ya zaɓi mataimakiyar gwamnan jihar Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, a matsayin abokiyar takararsa a zaɓen baɗi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Uba Sani ya fitar a daren Litinin ɗin makon nan.

Sanarwar ta ce, “Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina mai farin cikin sanar da cewa na zaɓi mai girma mataimakiyar Gwamna, Dakta Hadeeza Balarabe a matsayin abokiyar takarata a zaɓen gwamna na baɗi a jihar Kaduna.

Haka kuma ta cikin sanarwar ɗan takarar ya ce, “Dakta Hadiza Balarabe ta ba da gudunmawa sosai ga gagarumin ci gaba da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu a fannin samar da ababen more rayuwa da ci gaban jama’a a jihar.

“Dakta Balarabe ta nuna kwazo sosai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na mataimakiyar Gwamna wanda ya kara mata daraja a cikin masu ruwa da tsaki a jihar,” in ji sanarwar.

Haka kuma, Sanarwar ta ƙara da cewa, “Don haka ina kira ga al’ummar jihar Kaduna da su goyi bayan zabin Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata.

Uba Sani ya kuma ce, “Na buƙace ku da ku fito ranar zabe don kaɗa mana ƙuri’a yayin babban zaben baɗi da ke ƙaratowa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet