Labarai
Wata Gobara Ta Kone Shaguna Guda 30 A Bompai Da Ke Kano
Gobara ta kone wasu shaguna na wucin gadi guda 30 da masu aikin gyaran robar ke yi a Bompai da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ranar Talatar nan.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran waya da misalin karfe 3:30 na dare inda aka sanar da hukumar game da gobarar.
Abdullahi ya kara da cewa shagunan wucin gadi guda 30 masu girman kafa 1,000 da kafa 1,000, da ake amfani da su wajen gyaran roba gaba daya sun lalace.
Ya kuma bayyana cewa gaggawar da hukumar kashe gobara ta yi ta ceto injinan nika da ake amfani da su wajen narkewar roba daga konewa gaba daya.
Ya kara da cewa za a tantance musabbabin tashin gobarar daga baya. (NAN)
