Featured
Jami’an mu 1,500 ne za su yi aikin na musamman yayin bukukuwan Sallah – KAROTA
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta ce za ta tura jami’ai 1,500 wajen aiki a yayin gudanar da bukukuwan Sallah domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa a fadin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba.
A cewar sanarwar, an yi hakan ne don tabbatar da ingantuwar zirga-zirgar ababen hawa ga masu amfani da hanyoyi a lokacin bukukuwan Sallar.
Haka kuma sanarwar ta ce, “An umarci jami’an da su tabbatar da cewa masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanya sun bi duk dokokin jihar da suka shafi tuƙi da kuma amfani da titina domin magance cinkoson ababen hawa a lokutan bukukuwan.
“KAROTA ta yi gargadin cewa hukumar za ta kama tare da hukunta duk wanda ya karya dokar hanya a lokacin.
“Wasu marasa kishi sun mayar da su al’adar yin tuƙin ganganci a lokacin suna inda suke jefa rayuwarsu da ta wasu cikin haɗari,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa manajan daraktan Hukumar Baffa Babba-Dan agundi, na gargaɗin iyaye da su daina dabi’ar bai wa ƴa ƴansu masu karancin shekaru motoci su tuka musamman a wannan lokaci.
“Kamar yadda duk wanda aka kama yana tuki, za a kama shi, a ci shi tara sannan a kama motarsa kamar yadda kuma za a yi maganin tukin ganganci da wuce gona da iri.
“Sauran laifukan da suka shafi zirga-zirgar ababen hawa sun hada da rashin biyayya ga ababen hawa, wanda hukuncinsa a karkashin sashe na 16 4,7&8 (12) na dokar KAROTA 2012 wanda ya zo da tara,” in ji shi.
Ya kuma shawarci al’umma da su kiyaye duk dokokin zirga-zirga kafin bukukuwan Sallah da kuma bayan bukukuwan Sallah domin gujewa afkuwar haɗurran da ka iya jawo rauni ko asarar rayuka ko dukiya.
