Addini
Shugaban Hukumar NAHCON Ya bada Tabbacin Duk Mahajjatan Bana Zasu Je Aikin Hajjin
An ba da tabbacin jigilar dukkan maniyyatan da ke da niyyar zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2022.
Alhaji Zikrullah Hassan shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a birnin Makkah.
Ya ce Najeriya da sauran kasashen da ke fama da matsalar sufuri an kara wa’adin sa’o’i 24 daga kwanaki biyun da hukumomin Saudiyya suka bayar.
“Muradinmu ne kada a bar wani mahajjaci dan Najeriya a gida, kuma mun yi kokarin tabbatar da hakan. An yi sa’a, hukumomin Saudiyya sun kara tsawaita lokacin rufe sararin samaniyarsu.
“Da wannan tsawaitawar ne, sauran maniyyata 5,000 za su iya gudanar da aikin Hajjinsu. Sama da alhazai 1,000 ne ke kan hanyarsu a yau (Laraba). Wannan yana daga cikin 42,000 da suka yi rajistar aikin Hajjin 2022.
“Wadannan damammaki guda biyu; tsawaita lokacin rufewa da jigilar jiragen da aka yi hayar, zai tabbatar da cewa dukkan maniyyata sun tabbatar da burinsu na yin wannan aikin na addini,” inji shi.
Ya bayyana cewa kalubalen da aka fuskanta a baya sun kasance ne saboda sokewar da kuma tsaikon da ake yi na tashin jirage a sakamakon rashin shiri na jihohi.
A cewar Hassan, wadannan tsaikon su ne manyan dalilan da suka janyo tsaikon da ake samu a yawan jiragen da aka yi daga Najeriya zuwa yanzu.
Shugaban NAHCON ya bukaci ‘yan jarida da su rika nuna kwarewa a cikin rahotonsu na ayyukan Hajji na 2022.
KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa, Ya ce, an yi isassun shirye-shirye na raba ‘yan jaridan zuwa dukkan tantunan da ke wuraren Mai Tsarki domin baiwa ‘yan Najeriya isassun bayanai game da dukkan maniyyatan.
“Na fahimta da jami’in alhazan jihar Neja wanda ya damu da alhazan sa da ke Najeriya. Amma kamar yadda na bayyana masa, ina da hakki a kan sauran dimbin alhazan da tuni suke Saudiyya kamar na Najeriya.
“Wannan shine dalilin da ya sa na bar kwamishinonin Ayyuka, Shugaban Sufurin Jiragen Sama, Ayyuka na Musamman da sauran su don ci gaba. Sai aka yi sa’a, a lokacin da muka isa aka tsawaita sararin samaniyar,” inji shi.(NAN)
