Connect with us

Labarai

Gidauniyar Kidney Foundation ta buƙaci a riƙa taimaka wa masu ciwon Ƙoda

Shugaban gidauniyar Kidney Foundation mai rajin tallafa wa masu fama da ciwon Ƙoda, Architect Ibrahim Haruna, ya yi kira ga jama’a da su tallafa wa masu fama da larurar a duk inda suke domin kula da lafiyarsu kasancewar yana da tsada sosai.

Shugaban ya buƙaci hakan ne lokacin da yake miƙa gudummawar wasu kayayyakin da ake amfani da su na wankin Ƙoda watau Dialysis ga asibitin koyarwa na Abdullahi Wase da ke jihar Kano a Larabar makon nan.

Yayin gabatar da kayan, shugaban ya yi bayanin cewa gwamnati a matakin tarayya da Jihohi da kuma iyalan masu fama da cutar Ƙoda ba za su iya biyan kudin aikin wanki da sauran ɗawainiyar masu fama da cutar na yau da kullun ba saboda irin kuɗin da ake kashewa, Don haka ya yi kira da a tallafa musu ta duk hanyar da ta dace musamman da kuɗi don rage damuwar waɗannan Marasa lafiya.

Da yake karɓar kayayyakin, wakilin babban daraktan kula da lafiya na asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, Dakta Bashir Garba ya nuna jin dadinsa da wannan tallafin tare da bada tabbacin cewa kayayyakin da aka bayar za su taimaka matuƙa musamman wajen rage kuɗaɗen da ake kashewa a asibitin.

Da yake tsokaci, shugaban sashen wankin Ƙoda watau Dialysis na asibitin koyarwa na Aminu Kano Farfesa Aliyu Abdu da kuma mamba a gidauniyar Kidney Foundation sun shawarci mahukuntan asibitin koyarwa na Abdullahi Wase da su kai ziyarar neman shawarwari ga masu hannu da shuni a jihar Kano da kuma wajen jihar tare da duba don samun tallafi ga majinyatan su kamar yadda asibitin koyarwa na Aminu Kano ya yi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet