Labarai
Nasarawa: Ƴan sanda sun cafke ɗan Boko Haram da ya gudu daga gidan Yari na Kuje
Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, ta ce ta sake kama wani fursuna guda ɗaya da ya tsere a harin da ƴan ta’adda suka kai gidan gyaran hali na Kuje.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar PPRO Ramhan Nansel da ya fitar yau Asabar.
Sanarwar ta ce, jami’an ƴan sanda ne a garin Keffi suka cafke wanda ya tsere ɗin bayan samun bayanan sirri.
Haka kuma Sanarwar ta ce, “A ranar 9 ga Yulin bana da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar dare ƴan sanda a Keffi suka kama wani Hassan Hassan wanda sunansa da hotonsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere a harin ta’addancin Kuje.”
“Hukumar ƴan sanda ta bayar da umarnin miƙa wanda ake zargin zuwa wuri mafi tsaro yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda suka tsere.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a miƙa wanda ya gudu ga hukumar da ta dace domin daukar mataki.”
Ya kuma ce, Kwamishinan ƴan sandan jihar ya miƙa godiyarsa ga jami’an ƴan sanda a jihar bisa ƙoƙari da kuma aikin da suke yi.
