Labarai
Hukumar NDLEA ta cafke wanda ya tsere daga gidan gyara halin na Kuje tare da Wiwi
Jamian hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, sun cafke daya daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo da ya tsere daga gidan gyaran hali na Kuje, sakamakon harin da yan taadda suka kai gidan makon jiya a birnin tarayya Abuja.
A cewar hukumar jamian nata sun samu nasarar ne a yau Litinin.
Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar Mista Femi Babafemi, ya fitar.
Sanarwar ta ce, an kama wanda ake zargin ne Suleiman Sidi, da safiyar yau a a wani wurin shakatawa da ke Area 1, a babban birnin tarayya Abuja lokacin da yake yunkurin shiga motar haya domin zuwa birnin Maidugurin jihar Borno.
Femi ta cikin sanarwar ya kara da cewa an cafke shi ne tabar Wiwi.
Sanarwar ta kuma ce, Yayin da yake yaba wa jamian hukumar da kuma mutanen babban birnin tarayya Abuja bisa kamawa da kuma taka-tsantsan da suka yi, Shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa Mai Ritaya, ya bayar da umarnin a mika wanda ake zargin ga hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya NCoS.
