Allah ya yiwa guda daga cikin mutanen da suka fi daɗewa suna yi wa Masallacin Manzon Allah Tsira da Amincin su ƙara tabbata a gare shi hidima Malam Agha Habeeb Muhammad al-Afari rasuwa a yau Laraba.
BBC ta ruwaito cewa marigayin Agha Habeeb shi ne mai kula da ɗakin da kabarin Mazon Allah S.A.W yake.
Haka zalika ta ruwaito cewa an gudanar da jana’izarsa a masallacin Manzon Allah S.A.W da ke birnin Madina.
