Connect with us

Labarai

Ku yi amfani da lokacin Babbar Sallah wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya– Hon. Sagir Ibrahim koki

Ɗan takarar shugabancin majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni Kano KMC, Alhaji Sagir Ibrahim koki, ya taya al’ummar jihar Kano murnar bikin Babbar Sallah ta bana.

A wata sanarwa da ɗan takarar ya fitar a makon nan, ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su yi amfani da lokacin bikin Sallar wajen yin addu’ar samun zaman lafiya a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Alhaji Sagir Ibrahim koki, ya tabbatar wa al’ummar mazabar sa cewa idan Allah ya tabbatar da shi a wanan kujera zai kawo  nasarorin da samawa jama’a aiki kamar yadda ya Saba  jajircewar sa wajen ganin sun samu wakilcin da ya dace a zauren majalisar.

Ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su kiyaye kyawawan dabi’un Musulunci wanda ya ya koya wa mabiyansa ta yadda za su zauna lafiya ba kawai da ‘yan uwa musulmi ba, har ma mabiya sauran addinai.

Ɗan takarar ya ƙara da cewa, ba za a iya samun zaman lafiya da hadin kai a Najeriya ba, in ba tare da hakuri a tsakanin mabiya manyan addinai biyu na Musulunci da Kirista ba.

Bugu da ƙari, ya bukaci al’ummar musulmi da su rika nuna kauna da taimakawa ga makwabtansu da sauran jama’a, yayin da suke gudanar da bukukuwa irin wadannan masu muhimmanci a rayuwarsu.

Hon. Sagir Ibrahim koki, ya kuma yi fatan wannan lokaci na Sallah ya zama silar samun albarka, zaman lafiya, wadata da aminci ga ‘yan Nijeriya ganin cewa idan aka yi addu’a a wadannan kwanaki kalubalen da kasar nan ke fuskan ta za su zama tarihi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet