Connect with us

Tsaro

KAROTA: Za mu ci gaba da yin aiki da sashen MTD domin sauƙaƙa zirga-zirga

Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa KAROTA ta ce za ta ci gaba da yin aiki da Sashen Kula da binciken ababen hawa na rundunar ƴan sandan watau M.T.D domin sauƙaƙa wa masu ababen hawa wajen zirga-zirga.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa, ya fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta ce, Shugaban Hukumar ta  KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ne ya bayyana haka lokacin da yake karɓar baƙuncin sabon Shugaban sashen na M. T. D SP Abubakar Ibrahim Imam.

Baffa Babba ya ce hukumar KAROTA ba za ta iya gudanar da aikin ta ba sai da taimakon ƴan sanda, A saboda haka ne ya roƙi sabon shugaban da ya ruɓanya ƙoƙarinsa ga al’ummar jihar Kano ƙari akan ƙoƙarin da yake da shi.

A nasa jawabin Sabon shugaban sashen kula da ababen hawa SP Abubakar Ibrahim Imam ya bayar da tabbacin yin aiki tare da Hukumar ta KAROTA domin ciyar da jihar Kano gaba.

Ya bayyana cewa jami’an KAROTA na aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an Sashen domin taimakawa al’umma musamman masu amfani da titi.

Ya ƙara da cewa hadin kan da ke tsakanin jami’an Yansanda da jami’an na karota ne, hakan ya sa ake samun sauƙin cunkoso a titinan jihar nan.

Haka kuma ya yi alkawarin ci gaba da ɗora wa kan yadda ayyukan suke tafiya a tsakanin jami’an.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet