Uncategorized
Wani Jigo Kuma Dan Takarar Gwamna Ya Fice Daga Jam’iyyar APC
Wani jigo a jam’iyyar (APC) kuma dan takarar gwamna, Sanata Magnus Abe, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyya mai mulki.
Sanata Magnus Abe, wanda ya wakilci yankin Ribas ta Kudu maso Gabas a majalisar dokokin kasar har zuwa shekarar 2019, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar ga gidan talabijin na Channels a ranar Larabar nan.
A yayin da ake fama da rikicin cikin gida a jam’iyyar reshen jihar Ribas, ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne domin cimma burinsa na siyasa a wasu wurare.
Sanata Abe dai ya dade yana takun saka tsakaninsa da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar.
Bayan ficewar sa daga jam’iyyar, ya ki bayyana jam’iyyar da yake son shiga.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa bai mika takardar ficewa daga jam’iyyar ba domin sanar da shugabannin jam’iyyar ficewar sa.
Ya bayyana cewa a bisa tsarin mulkin jam’iyyar APC, duk wani memba na jam’iyyar zai daina aiki da zarar irin wannan mutum ya shiga wata jam’iyyar siyasa.
