Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Tarayya Za Ta Hana Tuka babura Na Acaba

Gwamnatin tarayya ta ce tana tunanin sanya dokar hana amfani da babura da aka fi sani da okada ko kuma achaba.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis din nan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa (NSC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ministan ya ce bincike ya nuna cewa ana amfani da baburan okada wajen aikin hakar ma’adanai a fadin kasar kuma haramcin na iya katse hanyoyin samun kudaden ‘yan ta’adda da ‘yan fashi.

Malami ya ce taron ya mayar da hankali ne kan kayan aikin da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki matakin saboda ‘yan ta’adda sun kaura daga hanyoyin da suka saba bi na samun kudaden gudanar da ayyukansu zuwa ma’adanai da karbar kudin fansa.

Ministan ya ce ’yan fashin ne ke amfani da baburan wajen motsi, yayin da hakar ma’adanai ke ba su kudaden da za su samu kudin sayen makamai.

Dangane da ko gwamnati za ta yi la’akari da illar hana babura da ayyukan hakar ma’adinai ga talakawan Najeriya da tattalin arzikin kasar, ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta fifita bukatun kasa da na jama’a fiye da bukatun mutum daya.

Shi ma da yake magana, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce an yi kokari sosai wajen tattara bayanan sirri kafin harin da aka kai a gidan yarin Kuje amma ya yi nadamar cewa babu yadda za a yi aiki da shi.

Aregbesola wanda ya ce an mika rahoton farko na bincike kan harin ga shugaban kasar, ya ba da tabbacin cewa za a bayar da cikakken rahoto a karshen binciken.

Ya ce za a hukunta wadanda aka samu sun yi watsi da aikinsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet