Ilimi
Yajin aikin ASUU: Muna Da Hakkokin Zanga-zangar, Shugaban NLC Ya Yiwa Lai Mohammed Martani
Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC, ta ce tana da hakkin ta yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da ci gaba da zaman daliban a gida, biyo bayan gaza cimma matsaya tsakanin mahukunta da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Shugaban NLC, Ayuba Wabba a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce “a sane ne da, ‘yancin yin taro cikin lumana da zanga-zanga wani hakki ne na duniya wanda kundin tsarin ‘yancin dan adam da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tabbatar.” .
Kalaman Wabba na zuwa ne a matsayin martani ga wata sanarwa da ministan yada labara da al’adu, Lai Mohammed, ya yi, inda ya nuna cewa zanga-zangar da kungiyar NLC ta yi na nuna goyon baya ga ASUU haramun ne.
Da yake mayar da martani, Wabba ya ce tattakin da ake shirin yi ba zanga-zangar hadin kai ba ne, ya kara da cewa kungiyar NLC na da hannu kai tsaye a rikicin da ke faruwa a jami’o’in kasar nan.
“Dukkan kungiyoyin kwadago hudu da abin ya shafa na NLC ne. Na biyu a matsayinmu na ’yan kasa, yaranmu sun yi watanni 5 ba su je makaranta ba, yawancin yaran ma’aikata ne kuma marasa galihu, wannan kadai ya kamata a dauki matakin gaggawa,” inji Wabba.
Ya jaddada cewa duk wani taro na lumana halal ne kuma baya bukatar wani izini a karkashin doka.
A cewarsa, a cikin al’ummar dimokuradiyya irin wannan magana da ministan ya yi bai dace da tsarin doka ba.
