Labarai
Neja: Ƴan sanda sun kuɓutar da mutane 9 daga hannun ƴan garkuwa
Rundunar ƴan sandan jihar Neja, ta ce, jami’anta sun kuɓubutar da wasu mutane tara da aka sace su a ƙauyen Kuchi da ke yankin ƙaramar hukumar Munya ta jihar.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Bala Kuryas, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Juma’ar nan a birnin Minna.
Kwamishinan ya ce, an sace mutanen ne a daren Alhamis ɗin makon da ta gabata.
Haka kuma ya ƙara da cewa, bayan kuɓutar da mutanen sun kuma sada su da danginsu.
Kwamishinan ƴan sandan na jihar Neja, ya nemi ƙarin goyon bayan mazauna jihar ta hanyar bai wa rundunar rahotonnin da za su taimaka musu wajen yaƙi da ɓata gari a ihar.
