Labarai
Za A Fuskanci Daukewar Wutar Lantarki Na Wasu Awanni A Yau — KEDCO
23/07/2022
*ZA A DAUKE HASKEN WUTAR LANTARKI NA WASU AWONNI DON GUDANAR DA WASU GYARE-GYARE*
Muna sanar da abokanan Hulɗarmu cewa za’a fuskanci ɗaukewar hasken wutar lantarki Yau 23 ga watan Yuli shekara ta 2022, sakamakon wasu yan gyare-gyare.
Ɗaukewar hasken wutar lantarkin na kimanin awanni takwas(8) zai fara ne daga misali karfe 10 na safe zuwa karfe 6 na yamma.
Ɗauke wutar zai ba damar gudanar da gyare-gyaren ne a Tashar da ake rarraba hasken wutar lantarki dake Kumbotso.
Muna roƙon abokan Hulɗarmu da su ƙara hakuri da zarar an kammala gyare-gyaren, kamfanin Kedco zai ci gaba da rarraba hasken wutar lantarkin kamar yadda ya sa ba.
Sanarwa:
Ibrahim Sani Shawai
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na KEDCO.
