Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutane 8 A Kaduna

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun ceto wasu mutane takwas da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Chikun ta jihar.

Jami’an ‘yan sandan da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Buruku, sun damke ’yan bindiga da dama a lokacin da suke sintiri a tsakanin kauyukan Udawa da Buruku da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari.

A cewar mai magana da yawun rundunar, Mohammed Jalige, ‘yan bindigar sun tare wasu motocin kasuwanci guda uku ta karfi, inda suka tafi da fasinjojin, suka nufi dajin.

Ya ce jami’an ‘yan sandan da suka ga gungun ‘yan ta’addan nan da nan suka fatattake su a yayin musayar wuta.

Ana cikin haka ne, Jalige ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun tsere zuwa cikin dajin da raunuka daban-daban, inda suka bar mutane takwas da aka yi garkuwa da su a baya.

Ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ya samu rauni kuma an kai su asibiti domin yi musu magani, yayin da wadanda aka ceto aka kai su ofishin ‘yan sanda da ke Buruku inda aka yi bayaninsu, aka kuma yi musu rakiya zuwa inda suke zaune.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaftar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

A ‘yan kwanakin nan dai ‘yan bindiga sun sake kai hare-hare a wasu sassan jihar Kaduna da wasu jahohin, inda ake kai wa limaman coci musamman mabiya darikar Katolika hari.

Daya daga cikin irin wadannan hare-hare na baya-bayan nan shi ne sace Reverend Father John Cheitnum da Reverend Father Donatus Cleopas a ranar Juma’ar makon jiya a karamar hukumar Jere ta jihar Kaduna.

Sace su ya zo ne makonni biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wani limamin cocin Saint Charles Catholic Church, Zamina a karamar hukumar Kauru.

Kwanaki bayan sace su, shugaban cocin Katolika na Kafanchan, Reverend Father Emmanuel Okolo, ya ce an gano gawar Cheitnum da ta rufta a ranar Talata.

A nasa bangaren, Reverend Father Cleopas, an ce barayin sun sako su ne bayan an biya su makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba a matsayin kudin fansa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet