Tsaro
Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe makarantun Sakandaren tarayya
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe makarantun Sakandaren tarayya watau FGC da ke Abuja.
Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar Mista Ben Goong, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan yau Litinin.
Ya ce, tuni ma’aikatar ta bada umarnin kwashe dalibai daga makarantun.
Rahotonni sun bayyana cewa ɗaukar matakin ya biyo bayan barazanar tsaro da makarantun na FGC ke fuskanta a babban birnin tarayya Abuja.
Hakan kuma ya biyo bayan harin da ƴan bindiga sun kai kusa da makarantar FGC Kwali a birnin tarayya Abuja.
