Labarai
Hukumar NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 175 da aka dawo da su daga Libiya
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta karɓi ƴan Najeriya ɗari da saba’in da biyar da ke yin ci rani a ƙasar Libiya kuma suka maƙale a can.
Hukumar ta ce, cikin mutanen da aka dawo da su ɗin a baya-bayannan sun haɗa da Maza casa’in da huɗu da kuma Mata tamanin da ɗaya.
Haka kuma hukumar ta NEMA, ta ce, ƙungiyar kula da yan ci rani ta duniya da kuma ƙungiyar tarayyar Turai ne suka ɗauki nauyin dawo da ƴan ci ranin gida Najeriya.
Hukumar ta ce a Janairun 2022, ta karbi ‘yan ci-rani kusan 2000 da suka komo daga Libya.
