Labarai
Sanatocin Jam’iyyun Adawa Sun Baiwa Shugaban Kasa Wa’adin Ya Kawo Karshen Matsalar Tsaro Ko Su Tsige Shi
Sanatoci daga jam’iyyun adawa sun ba shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida domin yakar matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Sun kuma yi barazanar fara shirin tsige shugaban kasar idan har ya kasa magance matsalar rashin tsaro a cikin wa’adin da ‘yan majalisar suka bayar.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Phillip Aduda, ya bayyana matsayin ‘yan majalisar a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a zauren majalisar a Abuja, babban birnin kasar.
